Israela zata rufe yankunan yan share guri zauna 12 a yammacin Gaza | Labarai | DW | 18.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israela zata rufe yankunan yan share guri zauna 12 a yammacin Gaza

Faraministan Israela, Ehud Olmert ya bayar da umarnin rufe wasu yankuna 12 da yan share guri zauna suka yi ka ka gida a cikin sa a yammacin Gaza.

Faraministan dai ya dauki wannan matakin ne bayan tuntuba da kuma amincewar ministan tsaron kasar,. Wato Amir Perez.

Daukar wannan matakin dai yazo ne kwanaki kadan kafin Ehud Olmert ya kai wata ziyara izuwa birnin Washinton don saduwa da shugaba Bush.

Idan dai za´a iya tunawa jim kadan bayan karbar rantsuwa a matsayin faraministan kasar, Ehud Olmert yayi alkawarin rushe matsugunan yan ka ka gida, wanda ya bayyana su a matsayin barazana ga harkokin tsaron kasar ta Israela.