ISIS ta kashe Yazidi 500 a cewar Bagadaza | Labarai | DW | 10.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ISIS ta kashe Yazidi 500 a cewar Bagadaza

Gwamnatin Iraki ta zargi kungiyar ISIS da kashe tsiraru mabiya addinin Yazidi da dama tun bayan da ta kaddamar da shirinta na kafa shari'ar Musulunci a kasar

Ministan kare hakkin dan Adam na Iraki ya bayyana cewar 'yan Kungiyar ISIS sun kashe tsirarrun mabiya addinin Yazidi 500 tun bayan da suka tayar da kayar baya a arewacin kasar. Mohamed Chia al-Soudani ya kara da cewa masu kaifin kishin addinin sun kuma binne wasu 'yan Yazidi da ransu ciki kuwa har da mata da yara kanana. Yayin da a daya hannun kuma suka kame wasu karin mata 300 da suka mayar bayinsu.

Mamaye wasu sassa na arewacin Iraki da masu fafatukar tabbatar da shari'ar musulunci suka yi, ya sa 'yan Yazidi da dama da kuma dubban Kiristocin kasar kaurace wa matsugunsu. Da ma dai 'yan Kungiyar ISIS sun dibar wa 'yan Yazidi 300 wa'adin yau Lahadi na su musulunta ko kuma suka kashesu.

Sai dai kuma a nata bangaren kasar Amirka ta kai farmaki a kan 'yan kungiyar ISIS a kwana na biyu a jere a arewacin kasar ta Iraki. Daga cikin abubuwan da suka lalata ha da motocin yaki na 'yan sunni da ke neman kafa shari'ar musulunci. Shugaba Barack Obama ya yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare ta sama a kan masu kaifin kishin addini, da nufin kauce wa abin da ya kira kisan kare dangi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo