IS ta rusa masallacin Al-Nuri a Iraki | Labarai | DW | 22.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta rusa masallacin Al-Nuri a Iraki

Rundunar sojojin Iraki ta sanar da cewar Kungiyar IS ta ragargaza masallacin Al-Nuri na garin Mosul, inda jagoran kungiyar Abu Bakr al Baghdadi ya ikirarin kafa Daula a shekara ta 2014.

Kungiyar ta IS ta musunta zargi kana kuma ta dora alhakin rusa masallacin da hasumiyar sa  a kan rundunar mayakan sama ta Amirka.  janar Al Saadi na daya daga cikin mayan kwamandojin sojin na Iraki: '' Muna a kan hanyar zuwa Mosul inda masallacin Al Nuri yake, za mu samu nasara a kan yan IS.'' Rusa masallacin wanda ke cike da tarihi wanda aka gina tun a karni na tara na zuwa ne a kwanaki na hudu na hare-haren da sojojin Irakin ke kai wa  a birnin na Mosul da nufin kwato shi daga cikin hannu 'yan tawayen.