IS ta dau alhakin hari a Pakistan | Labarai | DW | 08.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta dau alhakin hari a Pakistan

Kungiyar IS da ke fafutukar kafa daular musilunci, ta dauki alhakin hari kan wani asibitin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan.

Kungiyar IS da ke ikirarin jihadi na kafa Daular Musilunci, ta dauki alhakin hari kan wani asibiti da ke kudu maso yammacin kasar ta Pakistan. A safiyar wannan Litinin ce dai wani dan kunar bakin wake ya kusa kai cikin dandazon al'umma ya ta da Bam da ke jikinsa.

Wani babba jami'in asibitin Quetta ya ce alkaluman wadanda harin kunar bakin waken ya yi sanadiyayr mutuwarsu ya tashi daga 43 zuwa 66, mafi yawanci Lauyoyi yayin da likitoci ke ci gaba da ba da agajin gaggawa ga mutane sama da 100.