Iran tace ba za ta bayar da kai ba... | Labarai | DW | 20.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran tace ba za ta bayar da kai ba...

Shugaban addini Ajatollah Ali Khamenei na Iran ya jadadda a wani masallaci na birnin Teheran 'yancin da kasarsa ke da shi na gudanar da shirin nukiliya .

epa03634817 A handout picture made available by Iranian Supreme leader Ayatollah Ali Khamenei's official website shows Ayatollah Khamenei speaking to his audience during a ceremony in the city of Mashad, north-eastern Iran, 21 March 2013. Khamenei said he was not opposed to direct talks with the United States over the country's nuclear programmes but at the same time warned Israel of a military attack. 'The Zionists have threatened us with military attacks but if they dared and made such a mistake, then we would raze Tel Aviv and Haifa to the ground,' he added. EPA/KHAMENEI OFFICIAL WEBSITE / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES

Ayatollah Ali Khamenei

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fito fili ya bayyana cewa kasarsa ba ta da niyar dakatar da shirinta na nukiliya , sa'o'i kalilan kafin a koma kan teburin tattauna wannan batu a birnin Jeniva. Cikin wani jawabi da ya yi a gaban 'yan agaji dubu 50 da suka hallara a wani masallacin birnin Teheran, Khamenei ya jadadda 'yancin da kasarsa ke da shi na gudanar da shirin nukiliya na zaman lafiya.

Da ma tun da farko shugaba Barack Obama na Amirka ya ce kasarsa ba za ta yi gaggawar janye takunkumin karya tattalin arziki da ta kakaba wa Iran ba, sai idan ya ga yadda tattaunawa tsakaninta da kuma kasashen nan shida masu fada a ji a duniya ta kaya. Sannan kuma ya yi barazanar daukan matakin da ya dace idan taron na Jeniva ya wace ba tare da cimma matsaya ba.

A baya dai Iran da kuma kasashen nan biyar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus, sun cimma yarjejeniyar wucin gadi wacce ta tanadi dakatar da gina cibiyar nukiliya ta Arak da kuma dakatar da aikin inganta makamashin Uranium da Iran ta sa a gaba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu