Iran ta zargi makiya da ruruta rikicin kasarsu | NRS-Import | DW | 02.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Iran ta zargi makiya da ruruta rikicin kasarsu

C na kasar Ayatollah Ali Khamenei ya dora alhakin rasa rayukan mutane da raunata daruruwan akan makiyan kasar ta Iran wadanda suka haddasa boren ya ke neman zama babban tashin hankali

 Ayatollah Ali Khamenei, ya kuma kara da cewar makiyan kasar sun hada kai sun tanadi makamai da kudi har da tsaro, don su haifar da rikici a daular ta Islama, ya bayyana hakan ne a wata kafar sadarwar kasar.

Shugaban kasar ta Iran Hassan Rouhani ya yi kokari wajen kwantar da tarzomar, wadda ta fara da korafi akan tattalin arziki a ranar Alhamis, amma daga baya ta koma adawa ga shugabannin addinin a kasar, wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa. Masu adawar dai na fadin ''Mutuwa ga 'dan kama karya''.

A halin yanzu shugaba Rouhani ya dauki aniyar kawo karshen lamarin, inda ya bayyana a kafar sadarwar kasar cewar zai dauki matakin daya dace kan wadannan 'yan tsirarun da ke cin zarafin juyin juya hali.