1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi gwajin na'urar inganta Uranium

April 10, 2021

Iran ta ce ta fara yin gwaji kan wata sabuwar na'ura ta inganta sinadarin Uranium da ta samar wadda za ta iya yin aiki cikin gaggawa fiye da wadda take amfani da ita a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/3rpVg
Iran Hassan Rouhani und Ali Akbar Salehi
Hoto: Office of the Iranian Presidency/AP Photo/picture alliance

 

Tehran din ta ambata hakan ne dazu ta gidan talabijin din kasar mallakin gwamnati, inda ta ce gwaji kan sabuwar na'urar na daga cikin shirye-shiryen da aka yi yau na bikin Ranar Nukiliya ta kasar karo na 15.

Wannan gwaji da Iran din ta yi na sabuwar na'urar dai na zuwa ne daidai lokacin da ake fadi-tashi wajen ganin an farfado da yarjejeniyar nan ta Nukiliyar kasar da Iran din wasu kasashen duniya ciki har da Amirka suka cimma a cikin shekarar 2015.

Kasashen duniya dai sun mayar da Iran din saniyar ware saboda shirin nata na nukiliya wanda ake zargin tana amfani da shi wajen kera makaman kare dangi, zargin da bata sha musantawa inda ta kan ce shirin nata na zaman lafiya ne kuma tana yinsa ne don samar da makamashi.