1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta harba makami mai linzami

Ramatu Garba Baba
February 2, 2019

A wannan Asabar Iran ta kuma yin gwajin wani makami mai linzami a yayin da take kara fuskantar barazana daga kasashen duniya na aza mata karin takunkumai da ka iya haifar da nakassu ga tattalin arzikin kasa.

https://p.dw.com/p/3Cc1F
Symbolbbild Flugabwehrrakete
Hoto: Getty Images/AFP/S. Nachstrand

Makamin na daga cikin wadanda kasar ta kera a cikin kasa ba tare da taimakon wata kasa ba inji ministan tsaro Amir Hatami. Iran ta sha alwashin ci gaba da kera makaman da ake kallo na da hadarin gaske, duk kuwa da matsin da take fuskanta daga manyan kasashen duniya da kuma tarin takunkumin da ake aza mata.

Ministan ya kara da cewa, makaman da Iran ke kerewa an tanadesu ne don kare kasa daga duk wata barazana saboda haka babu bukatar su amince da duk wata doka ta kasa da kasa kafin yin abin da ya dace. Sai dai duk da haka,  ana kallon shirin kera makaman na Iran a matsayin barazana ga sauran kasashen duniya kamar Isra'ila da suke da tsamin dangantaka.