Iran ta yi barazanar sake kulle Mashigin Hormuz
April 18, 2026
Talla
Shugaba Donald Trump ya hakikance kan cewa, takunkumin da Amurka ta sanya kan jiragen Iran na hana su wucewa ta tekun Gabas ta Tsakiya zai ci gaba da kasancewa. Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce za a garkame mashighin idan har ba a cire takunkumin ba, wanda zai sanya jiragen ruwa sai sun tambayi izinin Iran din kafin su iya wucewa.
Karin bayani:Faransa da Burtaniya na tsara shirin bude mashigin Hormuz
Shugaba Trump ya kuma yi barazanar cewa zai janye daga yarjejeniyar bude wuta da Iran, idan har ba a cimma yadda za a kawo karshen yaki baki daya ba a ranar Laraba. A gefe guda ya yi ikrarin cewa Iran ta amince da bayar da sinadarinta na Uranium, sai dai kuma Iran din ta musanta hakan.