Iran ta saki sojan Amirka | Labarai | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta saki sojan Amirka

Sojan juyin juya hali na Iran sun sako sojan ruwan Amirka da suka tsare bayan da suka kutsa kai iyakarta ta cikin teku.

US-Marine-Seeleute in Iran

Sojan kundunbalar Amirka da Iran ta kama

Amirka ta bayyana cewa kasar Iran ta sako mata sojan ruwanta guda goma da ta kama bayan da suka kutsa kai iyakarta ta cikin teku ba tare da izini ba.

Dakarun sojan na Amirka suka ce sojan da mahukuntan na Tehran suka rike ya zuwa yanzu suna karkashin kulawar Amirka kuma babu wata alama a tattare da su da ta nuna cewa an taba lafiyar su.

Wannan bayani dai na zuwa ne bayan da kasar ta Iran ta bayyana sakin sojan a ranar Laraban nan inda suma a nasu bangaren sojan na Amirka suka fito tare da tabbatar da sakin nasu inda suka ce tuni ma dai sojan na Amirka suka bar sansanin sojan na Iran da ke tsibirin Farsi, inda a ka tsaresu karkashin kulawar sojan juyin-juya hali na Iran a jiya Talata.