1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na rikici da Birtaniya a tekun fasha

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2019

A cewar hukumomin Iran sun kama tankar man ne bayan hatsari da jirgin kamun kifi, kuma ana tsare da mutane 23 da ke cikin tankar a tashar jiragen ruwa na Bandar Abbas har sai an kammala bincike.

https://p.dw.com/p/3MMuz
Britischer Tanker Stena Impero
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Stena Bulk

Masu kula da gabar ruwan Iran sun ce a mashigin ruwan Hormuz a tekun fasha suka kwace tankar man, sai dai sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya gargadi Iran ta yi kuka da kanta idan har ba ta warware matsalar cikin lokaci ba.

Sabon rikicin ya kunno kai ne a dai-dai lokacin da Amirka ke ikirarin kakkabo wani jirgin yakin Tehran mara matuki da ke wa sojojinta barazana, ikirarin da gwamnatin Iran ta karyata.