1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Bunkasa a fannin tsaro da soja

Salissou Boukari
August 21, 2018

Kasar Iran ta gabatar da wani jirginta na farko na yaki wanda aka kera 100 bisa 100 a kasar, tare da jaddada karfinta na soja wanda ta ce makamai ne na kare kai da kuma neman zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/33UDQ
Iran Kampfflugzeug Kowsar
Hoto: Tasnimnews

Iran ta yi wannan gwaji ne a daidai lokacin da kasar ke zaman tankiya da Amirka. A cewar kamfanin sadarwa na kasar na Tasnim, jirgin yakin na Iran na dauke ne da kayayyaki na zamani ciki har da na'urar gano ko wane irin jirgi, sannan an yi gwajin jirgin yakin ne cikin nassara wanda wasu kafofin yada labaran kasar ta Iran suka wallafa.

Gidan talbijin na kasar ta Iran ya nuna shugaba Hassan Rohani zaune cikin jirgin yakin da aka radawa suna "Kowsar". Yayin wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar ta Iran, Shugaba Hassan Rohani ya ce idan ya na maganar karfinsu na kayan yaki ya na nufin suna neman zaman lafiya ne da sauran kasashen duniya, kuma ya kara da cewa idan har Iran ba ta nuna ta na da karfin da za ta kare kanta ba, to wasu kasashe na iya yi mata barazana har ma su shiga cikin kasarta da niyyar kai mata hari.