1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta fitar da sabon haramci ga wasu kasashe a Hormuz

March 27, 2026

Iran ta haramta zirga-zirgar jiragen ruwa a tsakaninta da kasashen da ke goyon bayan Amurka da Isra’ila, tare da gargadin daukar matakai masu tsauri ga duk wanda ya karya dokar.

https://p.dw.com/p/5BGB4
Jiragen dakon mai a Mashigar Hormuz
Jiragen dakon mai a Mashigar HormuzHoto: Altaf Qadri/AP Photo/picture alliance

Dakarun juyin juya hali na Iran sun sanar da haramta zirga-zirgar jiragen ruwa a tsakaninsu da tashoshin jiragen ruwa na kasashen da suke goyon bayan Amurka da Isra'ila.

Sanarwar da kafafen yada labarai ta gwamnatin Iran ta fitar ta ce an hana duk wani jirgi zirga-zirga zuwa ko kuma tasowa daga irin wadannan kasashe ta kowace hanya.

Haka kuma, dakarun sun jaddada cewa  mashigar ruwa taHormuza rufe take, suna masu gargadin cewa duk wani jirgin da ya yi yunkurin wucewa zai fuskanci matakai masu tsauri.

Karin bayani: Iran ta gindaya sharadin wucewa ta mashigar Hormuz

Rahotanni sun nuna cewa a wannan Juma'a, an mayar da wasu manyan jiragen daukar kaya guda uku na kasashe daban-daban da suka yi kokarin wucewa ta  mashigar Hormuz bayan sun samu gargadi daga rundunar ruwa ta Iran.

Tun bayan barkewar rikicin yankin, an takaita zirga-zirga a mashigar, duk da cewa ana barin wasu jiragen kasashe su rika wucewa.

A wani bangare kuma, kungiyar Houthi da ke Yemen ta ce a halin yanzu ba ta da shirin takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya, duk da hare-haren da ta taba kaiwa kan jiragen ruwa a baya.