1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Ba yaki ko wata tattaunawa da Amirka

Yusuf Bala Nayaya
August 13, 2018

Shugaban addinin a kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana a wannan rana ta Litinin cewa babu batun yaki ballantana tattaunawa tsakanin Iran da Amirka.

https://p.dw.com/p/33535
Iran Ali Chamenei während einer Rede in Teheran
Hoto: Reuters/Official Khamenei website

Khamenei ya bayyana haka ne a shafin Twitter inda ya ce a kwanannan Amirka na yawan magana kan kasar ta Iran kama daga batun kara wa Iran takunkumi ko batun yaki ko tattaunawa.

Akwai raderadi ko Iran za ta koma tattaunawa da Amirka bayan da kasar ta fice daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da aka cimma tsakanin kasar ta Iran da sauran kasashen yammacin duniya.

Kasar Iran dai ta ce babu batu na tattaunawa da Amirka, kasancewarta ba a bar aminta da ita ba bayan da ta fice daga waccen yarjejeniya.