Iran ta caccaki Birtaniya kan Hezbollah | Labarai | DW | 02.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta caccaki Birtaniya kan Hezbollah

Gwamnatin Iran ta caccaki matakin Birtaniya na sanya kungiyar Hezbollah cikin jerin kungiyoyin ta'addanci a duniya tare da yin watsi da yunkurin haramta rassan kungiyar.

Birtaniya ta ce a shirye ta ke ta haramta duk wata rassa na kungiyar Hezbollah da ke gudanar da ayyuka a sassa daban-daban a fadin duniya, matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amirka ta ayyana kungiyar Hezbollah cikin kungiyoyin ta'addanci na duniya bisa tasirinta a yankin gabas ta tsakiya. Shekaru 37 da suka gabata ne dakarun juyin juya hali na kasar Iran suka girka kungiyar Hezbollah da ke taka rawa a yakin da kasar Siriya ke yi da kungiyar IS.