Iran: Sababbin takunkuman Amirka | Labarai | DW | 24.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: Sababbin takunkuman Amirka

A hukumance Amirka ta kakabawa Iran sababbin takunkumai na tattalin arziki bayan barkewar takaddama kan kakkabo jirgin yakin kasar mara matukin da Iran din ta yi a makon da ya gabata.

Shugaban Amirka Donald Trump ya sanya hannu kan sababbin takunkuman na karya tattalin arziki ga Iran. Trump ya ce za su ci gaba da matsawa Tehran kaimi duk da taka tsan-tsan da suke yi na kaucewa afkuwar yaki da ita, sai dai ba wai hakan na nufin za a bar Iran din ta ci gaba da bunkasa makamashinta na nukiliya ba.

A wannan karon dai Trump ya ce takunkuman za su shafi ofishin jagoran juyyin-juya halin Musulunci na Iran din Ayatollah Ali Khamenei. Iran dai ta dogara ne kan albarkatun man da take fitarwa, ana kuma ganin matakin ka iya kara jefa tattalin arzikinta cikin mawuyacin hali.