1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran na shirye ta dakatar da yaki amman da sharadi

Abdoulaye Mamane Amadou
March 31, 2026

Gwamnatin Iran ta ce tana shirye ta kawo karshen yakin da take gwabzawa da kasasen Amurka da Isra'ila amma kuma idan an cika mata sharadi.

https://p.dw.com/p/5BSqb
Masud Peseschkian shugaban kasar Iran
Masud Peseschkian shugaban kasar IranHoto: Iranian Presidency/Anadolu/picture alliance

Iran ta ce a shirye take ta kawo karshen yakin da take gwabzawa da kasashen Isra'ila da Amurka, madamar ta samu wasu cikakkun hujjojin da ke nuna cewar ba za a sake yi mata sakiyar da ba ruwa ba.

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Tehran

Shugaban kasar da kansa Massoud Pezeshkian ne ya tabbatar da hakan, a yayin da yake zantawa da shugaban majalisar Turai Antonio Costa ta wayar tarho, inda Shugaba Pezeshkian, ya ce akwai damar tsayar da fadan da yanzu hakan ke cikin makonninsa na biyar, to amma kuma da sharadin cewar abokan gaba, ba za su sake yi wa kasar aika-aikar da suka yi mata a baya ba, mjusamman ma hare-haren da suka yi wa kasar mummunar barna a cewasa.

Amurka ta kaddamar da hari kan Isfahan

Tuni hannayen jarin Amurka suka fara tashi bayan jin wannan albishiri daga Iran, duk da yake a baya kakakin rundunar juyin-juya halin ya sanar da cewar a shirye kasar take da ta kai jerin hare-hare kan kamfanonin Amurka idan har ta kara kashe wasu daga cikin jiga-jigan kasar.