Iran na neman bai wa Saudiyya dauki | Labarai | DW | 25.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran na neman bai wa Saudiyya dauki

Mataimakin shugaban kasar Eshaq Jahangiri shi ne ya bayyana haka a yayin wani zaman majalisar zartarwar cewar za su ba wa Saudi Arabiya tallafi sakamakon hadarin da ya faru.

Mahukuntan kasar Iran sun bukaci Saudi Arabiya data sanya kasashen su cikin wani kwamitin bin ba'asin abi nda ya faru sakamakon fadowar wani karfe wanda ya haifar da turmutsutsu a inda mahajjata sama da dari 700 suka rigamu gidan gaskiyya ciki hadda Iraniyawa 131 yayin aikin hajjin banan.

Mataimakin shugaban kasar Eshaq Jahangiri shi ne ya bayyana haka a yayin wani zaman majalisar zartarwar kasar a jumma'ar nan, a inda ya kara da cewar kasashe irinsu Iran na daya daga cikin kasashen da suka fuskanci mawuyacin hali sakamkon iftila'in don haka kamata yayi a sanya ta cikin kwamitin bin kadin abin da ya faru.