Iran na kai hare-haren daukar fansa
March 18, 2026
A hare-haren da ta kai Isra'ila ta kashe babban jami'in tsaron ƙasar Iran, Ali Larijani da kuma shugaban rundunar Basij, Gholamreza Soleimani,wadanda suka mutu sakamakon abun da aka kira harin matsarota maciya amana kan gidan marigayin a lokacin da yake bacci.
An tsara fara bikin jana'izar ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana agogon ƙasar a dandalin Enghelab da ke Tehran. Haka kuma, za a haɗa da jana'izar ma'aikatan jirgin ruwa 84 da suka mutu bayan da Amurka ta nutsar da jirgin ruwan yaƙin Iran mai suna Iris Dena da makami mai linzami a ranar 4 ga watan Maris. Tuni dai babban hafsan sojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi barazanar ɗaukar fansa.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci jana,izar sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da gwagwarmaya kare kasarsu da kunyata makiyansu: "Zaton da makiyanmu ke yin a kasha jagororinmu kan zai durkusar da mu, juyin juya halinmu mai karfi nene da ba zai taba samun koma baya ba.
Rasha, wacce ta daɗe tana ƙawance da Iran, ta yi Allah wadai da mutuwar babban jami'in tsaron ƙasar Iran Ali Larijani, ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙasar, wanda aka kashe a wani hari da Isra'ila ta yi iƙirarin kai wa.