1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tehran na son a sakan mata mara

Ramatu Garba Baba
December 27, 2021

Iran ta yi kira ga manyan kasashen duniya a game da dage mata jerin takunkuman karya tattalin arzikin da suka sanya mata a kan shirin nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/44shC
Österreich | Atomgespräche mit dem Iran
Hoto: EU Delegation in Vienna/Handout/AFP

Gwamnatin Tehran ta nunar da cewa, babban abin da take bukata a yarjejeniyar shi ne, ba ta damar sayar da albarkatun man fetur dinta da kuma yin amfani da kudin kasar da ke bankunan kasashen waje. Takunkuman da aka kakabawa Iran kan man fetur da kuma kudin da ta ajiye a bankunan kasashen ketare, sun takura Tehran matuka, abin da ya sanya tilas take son cimma yarjejeniya da kasashen masu fada a ji a duniya kan makamashin nukuliyarta. 

Iran ta bukaci al'ummomin kasa da kasa, da su dage takunkumin da suka sanya mata a kan albarkatun man fetur dinta. Ministan harkokin kasashen ketare na Iran Hussein Amir-Abdollahian ne ya bayyana wannan bukata, yayin da aka koma kan teburin tattaunawa dangane da batun nukiliyarta a wannan Litinin.