1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Hukuncin kisa kan Shahram Amiri

Ahmed SalisuAugust 7, 2016

Hukumomi a Iran sun ce sun aiwatar da hukuncin kisa kan masanin kimiyar nan da ya kware wajen harkokin nukiliya wanda ya gudu zuwa Amirka a shekara ta 2009.

https://p.dw.com/p/1Jd1m
Iran Atomphysiker Shahram Amiri offenbar getötet
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Taherenareh

Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin ma'aikatar shari'ar Iran din ya ce an aiwatar da hukuncin kisa ne kan Shahram Amiri sakamakon leken asirin da ya yi wa Amirka tare da mika mata wasu bayanai masu muhimmanci wanda bai kamata a ce ta samu ba.

Ma'aikatar shari'ar ta ce a iya tsawon zaman da ya yi a gidan yari kafin a kashe shi, Amiri bai nuna wata nadama ta abinda ya aikata ba sai ma kokari da ya rika yi na gani ya aike wa Amirka wasu karin bayanan sirri duk kuwa da cewar yana daure.

Hukumomi a Iran dai ba su ambata hakikanin lokacin da suka kashe Amiri ba sai dai ana zaton yana daga cikin mutanen da aka kashe a ranar Talatar da ta gabata wanda gwamnatin kasar ta ce mutane ne da suka aikata manyan laifuka.