1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran: Dubban jama'a sun halarci sallar gawar Raisi

May 22, 2024

Al'ummar Iran sun fito kwansu da kwalkwatarsu domin halartar sallar gawar shugaba Ebrahim Raisi da ta jami'an gwamnatin kasar da suka rasu tare da shi a hadarin jirgi mai saukar Ungulu.

https://p.dw.com/p/4g85V
Iran | Trauer um Ebrahim Raisi
Hoto: Tasnim Agency

Dubun dubatar al'ummar Iran sun yi dandazo da sanhin wannan safiya ta Laraba a birnin Teheran domin girmama shugaban kasar marigayi Ebrahim Raisi da tawagar da ke marasa a lokacin da Allah ya karbi ransu a yayin hatsarin jirgi mai saukar Ungulu a ranar Lahadin da ta gabata.

Karin bayani: Zaman makokin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na Iran

Masu aiko da rahotanni sun ce jama'ar sun taru a jami'ar birnin Teheran inda jagoran juyin juya hali Musulumci Ayatullahi Ali Khameni ya jagoranci addu'o'in bankwana ga marigayi Ebrahim Raisi wanda ya mutu yana da shekaru 63 a duniya da kuma sauran manyan jami'an gwamnatin kasar da suka rasu tare da shi.

Ana sa ran wakillan kasashe da dama za su halarci jana'izar marigayi Raisi ciki har da wakilan Rasha da Turkiyya da kuma Iraki, sannan kuma shugaban Hamas Ismail Haniyey da mataimakin shugaban Hizbullah Naim Qassem suma za su kasance daga cikin wadanda za su mahalarci jana'izar.