1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban addini a Iran ya bayyana muhimmancin kada kuri'a

Zulaiha Abubakar
February 21, 2020

Al'ummar Iran sun fito don zaben 'yan majalisar dokoki a wannan Jumma'ar, jim kadan bayan da jagoran addini Imam Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana muhimancin zaben ga masu kaunar kasar.

https://p.dw.com/p/3Y6mP
Iran Parlamentswahl Ajatollah Chamenei
Hoto: picture-alliance/dpa/ Office of the Iranian Supreme Leader

Masana siyasa a kasar Iran na ganin cewa haramta wa wasu 'yan siyasa da yawansu ya kusan 9,000 masu akidun kawo canji  shiga takarar kujerun zauren majalisar dokokin zai yi tasiri wajen fitar 'yan tsirarun mutane domin kada kuri'u a cibiyoyin zabe.

Zaben 'yan majalisar dokokin na gudana ne a lokacin da tattalin arzikin kasar Iran ke fuskantar kalubale sakamakon takunkumi da kuma wariyar da kasar ke fuskanta a bangaren diplomasiyya. Kusan 'yan takara dubu bakwai ne daga mazabu 208 suke neman zamowa wakilai a kujeru 290 na zauren majalisr dokokin kasar ta Iran.