Iran: Ana ta kama masu zanga-zanga | Labarai | DW | 14.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: Ana ta kama masu zanga-zanga

A kalla mutum 30 daga ne cikin masu zanga-zangar Allah wadai da harbo jirgin saman fasinja mallakar kasar Ukraine da kasar Iran ta yi a satin daya gabata aka kama a wannan rana ta Talata.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun masu shari'a a kasar Gholamhossein Esmaili.
A yau Talata Esmaili ya sanarwa manema labarai cewar an gudanar da bincike wanda ya kai ga kame mutane.

Jirgin saman mallakar kasar Ukraine da Iran din ta harbo ya janyo asarar rayukar sama da mutum dari da sabain, wanda da farko Iran din ta musanta zargin da wasu kasashen duniya ke mata kafin daga bisani ta amince wanda ta ce hakan ya faru ne bisa kuskure.