1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kashe wasu masu yada kyamar Musulunci

Ramatu Garba Baba
May 8, 2023

Iran ta kashe wasu mutane biyu da ta yanke wa hukuncin kisa a baya, bisa laifin yada farfaganda na nuna kyamar addinin Musulunci a shafukan intanet.

https://p.dw.com/p/4R2UH
Kasashen yamma na adawa da hukuncin kisa
Kasashen yamma na adawa da hukuncin kisaHoto: Christoph Hardt/Geisler-Fotopress/picture alliance

Iran ta kashe wasu mutane biyu da ta yanke wa hukuncin kisa a baya, bayan samunsu da laifin yin batanci ga addinin Musulunci. Kamfanin dillancin labaran kasar mai suna Mizan ne dai ya wallafa labarin a shafinsa na yanar gizo a wannan Litinin, amma ba tare da baiyana takaimaimen ranar da aka aiwatar da kisan ba.

Kamfanin ya nuna cewa, mutanen da aka aiwatar da kisan kansu, sun hada da Yousef Mehrdad da Sadrollah Fazeli Zare, sun kuma jima suna amfani da shafukansu na yanar gizo a wallafa ra'ayoyi na batanci da kuma yada kyamar addinin Islama, laifukan da suka saba wa dokokin kasar ta Iran.