Iran: An kare tsawaita wa′adin tattaunawa | Labarai | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: An kare tsawaita wa'adin tattaunawa

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya kare dalilan tsawaita wa'adin tattaunawa da ake yi kan shirin nukiliyar Iran da ke cike da takaddama.

John Kerry ya ce tsawaitawar a wannan gaba ya yi daidai saboda irin kyakkyawan cigaba da aka samu inda a hannu guda ya nemi 'yan majalisar wakilan Amirka da kada su kakabawa Tehran karin takunkumi ganin cewar an gaza cimma matsaya kafin cikar wa'addin da aka diba.

Mr. Kerry ya ce maimakon karin takunkumi kamata ya 'yan majalisar su baiwa gwamnatin kasar hadin kai ta fuskar bada karin lokaci na tattaunawa da Iran din don a kaiwa ga cimma matsaya ta dindindin domin bai kamata a yi watsi da irin matsayin da aka kai yanzu ba.