Iraki ta nemi tallafin Kungiyar NATO
December 4, 2014Gwamnatin Iraki na bukatar kungiyar tsaro ta NATO ta tallafa mata a wajen inganta harkokin sojanta a hukumance.
Amirka dai tuni ta shiga aikin ba da horo ga dubban mayakan kasar mafi akasari a yammacin lardin Anbar.
A yayin da ya halarci taron birnin Brüssel a ranar Laraba Firaminista Haider al-Abadi ya ce kasar Iraki ta kasance kasa daya tilo da ta shiga yaki da mayakan IS a yankin Gabas ta Tsakiya ba kakkautawa.
Wakilin DW a yayin taron na Brüssel Max Hoffmann ya ce akwai ci gaban ingantar dangantaka tsakanin mahukuntan na Iraki da kasashen yamma.
Ya ce wani abin da ke zama nasara a yayin wannan taro na zama yadda sabon Firaministan kasar ta Iraki da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry suka tabbatar da cewa lamura na ci gaba da sauyawa tsakanin kasashen kuma akwai ci gaba da ake samu bayan da sabuwar gwamnatin ke tafiya da kowane bangaren addini a gwamnatin kasar ta Iraki.