Iraki na cikin tashin hankali
Matsalar rashin aikin yi da ta cin hanci: Tsawon kwanaki dubban al'ummar Iraki ke zanga-zanga. Dokar hana zirga-zirga ba ta hana su yin zanga-zangar ba. Gwamman mutane sun rasa ransu, sama da 1600 kuma sun jikkata.
Ranakun tashin hankali
Duk da alkawarin kawo gyara daga gwamnati, zanga-zangar nuna adawa da cin hanci da matsin tattalin arziki, na ci gaba a Iraki. Ko da a ranar Jumma'a, mutane sun taru a wasu wurare da ke tsakiyar Bagadaza babban birnin Irakin, haka ma a kudancin kasar.
Ba a daina zanga-zangar ba
Ya kamata dokar hana zirga-zirga da aka sanya bayan kwashe kwanaki ana bata kashi ta sanya al'amura komawa daidai. Ofishin hukumar kare hakkin dan Adam a Bagadaza ya ce kimanin mutane 38 ne suka halaka, 35 daga cikinsu masu zanga-zangar ne yayin da wasu 1600 suka jikkata. Masu zanga-zangar da dama sun bijirewa dokar hana zirga-zirgar, inda suke kwana a kan tituna.
Zanga-zanga ba tare da jam'iyya ba
Zanga-zangar ta sha bamban da ta halin kuncin rayuwa da aka saba yi a Iraki. A wasu yankunan ana samun hasken wutar lantarki na tsawon sa'o'i hudu kacal a rana. Babban bankin duniya ya ce kaso 25 na matasan kasar ba su da ayyukan yi. Babban malamin Musulmi mabiya mazhabar Shi'a a Irakin Ali al-Sistani ya yi kira da a gudanar da gagarumar kwaskwarima a harkokin gudanarwa kafin lokaci ya kure.
An rufe ko ina
Da fari an shirya yin zanga-zangar ba tare da tuta ko katuna dauke da rubutu ko kuma taken wata jam'iyya ba. Sai dai abubuwa sun rincabe bayan korar wani fitaccen janar na soja Abdel-Wahab al-Saadi. A Bagadaza, masu zanga-zangar sun yi kokarin shiga wani yanki da ake kira da "Green Zone." A wannan yanki da ke cike da tsaro, akwai ofisoshin gwamnati masu yawa da ofisoshin jakadancin kasashen waje.
Zargin 'yan sanda da cin zarafi
Jami'an tsaro na amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar. Ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, ya zargi 'yan sanda da amfani da harsasai na gaske da na roba. An soki firaminista Adel Abdel Mahdi bisa yabawa jami'an tsaron da ke amfani da karfi wajen murkushe zanga-zangar da kuma dora alhakin cin zarafin kan wasu mutane da bai bayyana ba da ya yi.
Kira domin yin taka tsan-tsan
Shugaban kasar Iraki, Barham Saleh (Hoto, Maris 2019), ya yi tir da tashe-tashen hankulan tare da bukatar yin taka tsan-tsan da kuma bin doka. Saleh ya nunar da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da damar yin zanga-zangar lumana. Kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dokokin Irakin, ya yi tir da matakin murkushe masu zanga-zangar da karfin tuwo.