Zanga-zangar neman sauyi a Iraki
January 31, 2020Talla
Masu zanga-zangar dai na neman a sauke gwamnatin da suke zargi da cin hanci. Sun kuma bukaci a kawo karshen katsalandan din da kasashen ketare ke yi a kasarsu, tun bayan da rundunar taron dangi karkashin jagorancin Amirka ta kifar da gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar marigayi Saddam Hussein a shekara ta 2003. Rahotanni sun nunar da cewa kimanin mutane 500 ne suka halaka tun bayan fara zanga-zangar ta baya-bayan nan, da ta rikide zuwa tashin hankali a Irakin.