Iraki: Jingine aiyukan jakadancin Amirka
January 1, 2020Talla
Masu zanga-zangar dai sun mamaye harabar ofishin jakadancin kasar ta Amirka ne tare da jefa duwatsu da kokkona wasu muhimman kayayakin kasar da ke ga jikin ma'aikatar ta huldar jakadancin Amirka a Bagadaza, ciki har da Kyamarori masu daukar hoto daga nesa.
Wata sanarwar da ofishin jakadanci kasar Amirka ta fitar ta shawarci ma'aikatan ofishin da su gujewa zuwa ma'aikatar kana kuma ta dakatar da duk wasu alkawulan tattaunawa ko na bayar da visa da ta daukarwa jama'a.
Tuni wasu rahotanni daga birnin Washington ke cewa babban sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya bayyana matakin dage kai ziyarar aiki a kasar Ukraine biyo bayan kai harin ga ofishin jakadancin Amirka a birnin Bagadaza.