IRAKI AYAU ALHAMIS. | Siyasa | DW | 19.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

IRAKI AYAU ALHAMIS.

Gwamnatin Iraki ta bawa Muqtada al -Sadr da magoya bayansa waadin Saoi......

Moqtada al-Sadr da magoya bayansa.

Moqtada al-Sadr da magoya bayansa.

Gwamnatin kasar Iraki ta bawa limamin shiawa Muqtada al-Sadr,waadin saoi kalilan na kawo karshen fadan dake cigaba da gudana,tare da kwance damarar mayakansa,a hannu guda kuma da ficewa daga wannan masallaci mai tsarki dake garin Najaf,ko kuma ya fuskanci fushin sojin kasar.

A birnin Bagadaza,dakarun Amurkan ayau sun afakawa birnin Sadr da tankunan yaki,inda suka fuskanci martani daga Shiawan amma ba mai tsanani ba.kakakin Sadr yace ,Limamin nasu na bukatar a tura masa mai shiga tsakani wanda zasu tattauna yadda zaa kwance damarar yakin daya dauki makonni biyu yana gudana a garin na Najaf,fadan daya zubar da darajan gwamnatin prime minista Iyad Allawi,baya ga daruruwan mutane da suka rasa rayukansu.Sadr din dai na bukatar Jakada na musamman da zasu tattauna tabbatar da yarjejeniyar bukatunsu kann wannan rikici.

Karamin ministan Iraki kasim Daoud ya fadawa taron manema labaru a garin Najaf cewa ,gwamnati tabi dukkan hanyoyi dasuka dace na warware wannann rikici cikin lumana amma yaci tura,inda zabin karshe daya rage mata shine amfani da karfin soji,idan har shi Sadr bazai mika wuya tare da ficewa daga masallacin saydina Ali da magoya bayansa ba.

Minister Dawoud yace Limamin Shiawan na cikin waadin saoinsa na karshe,kafin a afka masa da karfin Soji,saidai yaki ambaton yadda sojojin zasu afkawa wannan masallaci mai tsarki wa yan Shia,inda kuma nan ne Sadr da magoya bayansa ke fake.

Kowane irin hari aka afkawa wannan wuri mai tsarki na iya muzantawa sauran Shiawa ,wadanda sune mafi rinjaye,musamman ma idan sojin Amurka suka kasance ciki.Da safiyar yau a garin na Najaf dai anji gurnanin tashin boma bomai da harbin bindigogi a yankin kudancin birnin.A jiya nedai Sadr ya amince da barin wannan masallaci da magoya bayansa,idan an cimma yarjejeniya da kimanin sojin Amurka da tankunan yaki 2,000,dake kewaye da wannan birni.

A jiya ne aka cimma batun tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu a wajen taron kasa daya dauki yini 4 yana gudana a birnin Bagadaza,taron daya tattara fitattun yan iraki sama da 1,000,wanda ake ganin cewa wata tudun dafawace a democradiyyar wannan kasa.An dai kammala taron da zaban wakilai 81,zuwa sabuwar majalisar Irakin.Ayayinda sauran 19,zaa nadasu ne daga majalisar wakilai da Amurka ta nada a baya,wadanda kuma basu samu shiga gwamnatin rikon kasar na yanzu ba.

A yayinda ake cigaba da dauki ba dadi a garin na Najaf,a yau ne kuma gidan talabijin din Aljazeera ta gabatar da wani vedio dake bayyana wasu yan kungiyan sa kai dake kiran kansu Martyrs Brigade,wadanda kuma suka lashi takobin kashe wani dan jaridan yammaci Micah Garen daya bace a garin Naziriyya tun ranar jummaar data gabata,idan har dakarun Amurka basu fice daga najaf ba cikin saoi 48.

A birnin Hillah dake Irakin kuwa,dakarun Poland 2 suka rasa rayukansu ,ayayinda wasu 5 suka samu raunuka sakamakon kwanton bauna da akayiwa motar da suke tafiya ciki.Kazalika wasu yan bindiga dadi sun harbe wani jammiin tsaron kamfanin man Iraki tare da raunana wasu biyu a garin Kirkut dake arewaci.Bugu da kari a gidan kurkukun Abu Ghraib ,sojin Amurka sun bindige prisononi 2 tare da raunana wasu 5,a wani yamutsi daya barke tsakanin mazauana wannan gidan yari.

A hannu guda kuma bayan taron nadin yan majalisar dokokin Irakin a taron daya kare jiya,An kebe ranar 1 ga watan Satumba a matsayin ranar zamanta na farko a wannan kasa.Ana dai saran wakilan majalisar zasu bawa gwamnatin rikon kwaryan shawarwari dangane da yadda zata gudanar da zaben kasa dazai gudana a Irakin a watan janairu 2005,idan mai duka ya kaimu.Halin da Iraki ta wayi gari ciki kenan a yau Alhamis.

Zainab mohammed

 • Kwanan wata 19.08.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvhA
 • Kwanan wata 19.08.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvhA