Iraki: An kammala zaben majalisar dokoki
May 12, 2018Talla
An gano biyu daga cikin mamatan wadanda suka fito yin zabe ne yayin da guda ya kasance daya daga cikin masu sa ido kan zaben. Kungiyar IS da ta yi alkwarin kai hari a yayin wannan zaben, ta dauki alhakin kai harin amman kawo yanzu babu tabbacin hakan daga hukumomin kasar.
Wannan zabe shi ne irinsa na farko tun bayan da kasar ta ayyana samun nasara kan 'yan kungiyar da ke da'awar jihadi kuma ana kallon zaben a matsayin wani zakaran gwajin dafi na farin jinin firaministan kasar Haider a-Abadi. Masu aiko da rahotanni sun ce kimanin 'yan takara dubu bakwai daga jam'iyyu daban-daban na kaasar ne ke zawarci kujerun majalisar dokokin kasar guda dari uku da ashirin da tara.