1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fahimtar juna tsakanin addinai

Mohammad Nasiru Awal AH
February 6, 2019

Paparoma Francis ya yi fatan ziyarar da ya kai yankin kasashen Larabawa za ta karfafa hulda da Musulunci.

https://p.dw.com/p/3CpmM
Papst Franziskus in Abu Dhabi
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Hamdy

Paparoma Francis ya fada a wannan Laraba cewa yana fata ziyara ta tarihi da ya kai kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za ta taimaka a kawar da rashin jituwa tsakanin addinin Kirista da na Musulunci.

A taron da ya saba yi a kowace ranar Laraba shugaban na mabiya darikar Katholika a duniya ya yi nuni da wata muhimmiyar yarjejeniya da suka rattaba wa hannu da babban limamin masallacin Azhar kuma babban malamin jami'a Sheikh Ahmad el-Tayeb lokacin da fafaroman ya kai ziyara a yankin tsibirin kasashen Larabawa.

Paparoman ya ce a zamani irin namu, inda akwai babbar fargabar yin fito na fito tsakanin addinin Kirista da na Musulunci, inda kuma ake kallon addinai da zama umul-aba'isun tashe-tashen hankula, muna son mu aike da babban sako da zai kawar da wannan zargi wanda kuma zai nuna cewa akwai damar girmama juna tare da shiga tattaunawa duk da bambamce bambamcen da ke akwai.