1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta sanya ranar daina rajistar katin zabe

Uwais Abubakar Idris ZUD
July 15, 2022

Sanarwar ta INEC dai na zuwa ne a yayin da masu sharhi ke nuna yadda akasarin jihohin kudancin Najeriya suka zarta jihohin arewacin kasar karbar katin na zabe, duk da cewa yankin arewacin ya fi kudancin yawon al'umma.

https://p.dw.com/p/4EDeC
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta sanar da karshen watan nan a matsayin lokacin da za ta kawo karshen aikin sabuntawa da karbar katin zaben da za a yi a shekara mai zuwa. Matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na  ci gaba da rijistar masu jefa kuri’ar, inda kotun ta ce hukumar zaben na da ikon dakatar  da aikin.

Tun da farko kungiyar SERAP mai faftukar kare 'yancin dan Adam ce dai ta shigar da karar domin dakatar da hukumar INEC rufe aikin rajistar masu zaben a karshen watan da ya gabata.