1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indonesiya: Prabowo Subianto ya yi ikrarin lashe zabe

February 14, 2024

Ministan tsaron Indonesiya, Prabowo Subianto ya yi ikrarin samun nasara lashe kujerar shugaban kasa a zaben da ya gudana a kasar.

https://p.dw.com/p/4cP5x
Dan takarar shugaban kasar Indonesiya Prabowo Subianto
Dan takarar shugaban kasar Indonesiya Prabowo SubiantoHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Sakamakon farko-farko da ba a hukumance ba sun yi nuni da cewa Subianto na kan gaba da kashi 60 cikin 100 a zagayen farko na zaben, inda Anies Baswedan da ke kasancewa tsohon gwamnan jihar Jakarta ke biye masa da kashi 25.

Zaben Indonesiya na wannan Larabar na zama zaben rana guda mafi girma a duniya. Prabowo wanda tsohon janar din soja ne ya kasancewa daga cikin wadanda suka yi zamani a lokacin mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Suharto, kana ake ganin shi ne zai gaji shugaba Joko Widodo da ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu.