SiyasaIndonesiya
An bude runfunan zaben a Indonesiya
February 14, 2024Talla
Al'umma ta fara kada kuria a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Indonesiya,inda ake sa ran kimanin mutane miliyan 205 za su kada kurii'a. 'Yan takara guda uku ne dai za su fafata a zaben a ciki har da ministan tsaro na yanzu Prabowo Subianto,tsohon janar na soji. Ko da yake ana zarginsa da take hakkin dan Adam a karkashin mulkin kama-karya na Suharto a karshen shekarun 1990, Amma dai ana ganin tsohon janar din mai shekaru 72 na iya yin nasara a zagayen farko na zaben domin ya gaji Joko Widodo wanda ya kammala wa'adinsa biyu.