1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indonesiya na neman agajin duniya

October 1, 2018

Masu aikn ceto na binne darurwan wadanda girgizar kasa da ma guguwar tsunami suka kashe a Indonesiya.

https://p.dw.com/p/35m1V
Indonesien Das Roa-Roa Hotel auf Sulawesi nach dem Erdbeben
Hoto: REUTERS

Sama da kaburbura dubu guda ne masu aikin ceton suka samar inda za a binne wadanda girgizar kasa da ma guguwar tsunami da kasar ta fuskanta suka halaka.

Hukumomi sun ce ana binne mutanen ne saboda kauce wa yaduwar wasu cututtuka daga gawarwakin da ke baje a wuraren da abin ya auku.

Gwamnatin kasar dai a yanzu na yekuwar neman daukin kasashen duniya dangane da ibtila'in da ta afka wa yankinta na Sulaweisi.

Alkaluman mahukuntan na cewa akalla mutum 840 ne suka salwanta a lamarin, sai dai suna iya zarta hakan; ana kuma ganin kasar ba za ta iya daukar nauyin da ya hau kanta ba.

Tuni dai Shugaba Joko Widodo, ya bude gidauniyar neman tallafin kasashen na duniya don ganin yadda za a tinkari lamarin.

Wasu sabbin rahotannin na cewa wasu fursunoni da dama sun tsere daga gidajen yarin da suke tsare a yankin da girgizar kasar ta faru a cikinsa.