Indonesiya: Hukuncin kisa kan dan kungiyar IS | Labarai | DW | 22.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesiya: Hukuncin kisa kan dan kungiyar IS

Wata kotu a birnin Jakarta na kasar Indonesiya ta yankewa wani Malami mai tsatsauran ra'ayin adinin Musluncin hukuncin kisa a wannan Juma'a, bayan da aka same shi da laifin bada izinin kai wasu jerin hare-hare.

A kasar a shekara ta 2016 ne dai wannan Malami mai suna Aman Addurrahman ya bada izinin kai wani hari a kasar ta Indonesiya, wanda ke a matsayin hari na faro da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa a wannan kasa da ke yankin Kudu maso gabashin Asiya.

Kotun dai ta samu babban malamin mai wa'azi a kasar mai suna Aman Addurrahman da laifin kitsa hare-haren da aka kai a kasar da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, wanda a cikinsa maharan guda hudu suka mutu.

Shugaban kotun mai suna Akhmad Zaini, ya kara da cewa an sami wannan malamin kuma da hannu cikin wasu hare-hare da aka kai a kasar. Sai dai Malamin da ke zaune ya yin yanke masa hukuncin bai nuna wani yanayi na nadama ba.