1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Jam'iyyar PTI ta lashe zabe

Ramatu Garba Baba
July 27, 2018

Imran Khan tsohon zakaran wasan Kirket kana shugaban jam'iyyar PTI na Pakistan ne ya lashe zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a kasar.

https://p.dw.com/p/329Im
Pakistan Islamabad Politiker Imran Khan
Hoto: Reuters/A. Perawongmetha

Hukumar zaben kasar ECP ce ta bayyana sakamakon zaben a wannan Juma'a. Imran Khan ya godewa miliyoyin magoya bayansa,  inda ya ce nasarar ba ta jam'iyyarsa ta PTI kadai ba ce, ta al'ummar kasa ce baki daya, ya ja hankulan a yayin da ya soma da yi wa 'yan kasar alkawarin kiyaye dukiyar kasa da rage almubazzuranci a cikin gwamnati da kuma alkawarin magance matsaloli na tsaro sai batun neman sulhu da makwabciyar kasar wato Indiya a jawabinsa ga manema labarai.

Jam'iyya mai mulki ta  PML-N ta yi watsi da sakamakon zaben tana mai zargin an tafka magudi a cikinsa. Amma Khan ya mayar da martani inda ya sha alwashin kaddamar da bincike kan wannan zargin. Rashin samun  rinjaye na kujerun 'yan majalisar dokoki na daya daga cikin kalubalen da sabon firaiminstan zai fuskanta, jam'iyya mai mulki dai ta yi nasarar samun kujerun 'yan majalisun 127 daga cikin 297 yayin da jam'iyyar PTI ta Imran Khan ta samu 117 abin da ke nufin sai ya nemi kulla kawance kafin kafa gwamnati.