Illar rashin tsabtar muhalli ga lafiya | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Illar rashin tsabtar muhalli ga lafiya

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewa babban abin da ke haddasa cututtuka da ma rashin abinci mai gina jiki shi ne rashin tsabtar muhalli.

Ban ya ce wannan batu dai shi ne na rashin tsabtar muhalli da kuma samun abinci mai tsabta. Ban ya bayyana hakan ne a wannan Alhamis, a yayin bikin tunawa da ranar bandaki ta duniya da aka saba gudanarwa a ranakun 19 ga watan Nuwamba na ko wacce shekar. A kiyasin Majalisar Dinkin Duniya dai sama da mutane biliyan biyu na zaune ne a muhallin da ba shi da tsabta, yayin da kusan biliyan guda ba su da bandaki a duniya suna yin bahaya ne a wuri budadde. Ban ya kara da cewa rashin tsabtar muhalli na daya daga cikin muradun ci gaban karni na majalisar wanda ya zo karshe a wannan shekara da muke ciki da al'ummomin kasa da kasa suka gaza cimma.