1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICJ ta yi watsi da bukatar karin kariya ga Falasdinawa

February 17, 2024

Kotun Duniya ta yi watsi da bukatar kasar Afirka ta Kudu na samar da karin matakai domin bayar da kariya ga Falasinawa gabanin farmakin da Isra'ila ta shirya kai wa Rafah.

https://p.dw.com/p/4cVuh
Kotun Majalisar Dinkin Duniya
Kotun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

A watan Janairun da ya gabata ne kotun ICJta umurci Isra'ila kan ta dauki dukkanin wasu matakan da zai hana dakarunta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Zirin Gaza, karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar.

Karin bayani: Kotun MDD zata fara shari'ar Pretoria da Isra'ila kan Gaza 

Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, kasar Afirka ta Kudun ta sake shigar da karin koke na neman daukar sabin matakan dakile shirin Isra'ila a Rafah. Kotun ta ce  hare-haren na kara jefa yankin cikin bala'i da dama yaki ya daidaita, sai dai bata bayyana wasu matakai da za a dauka ba. Hukuncin da aka yanke ya kuma nuna cewa Isra'ila har yanzu bata kammala sauke nauyin da ke kanta ba karkashin dokar hana kisan kare dangi.