ICC: Dan tawayen Kwango Ntaganda zai san makomarsa | Labarai | DW | 30.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC: Dan tawayen Kwango Ntaganda zai san makomarsa

Kotun hukunta masu aikata muggan laifuka ta  kasa da kasa , ICC, za ta yanke hukunci a wannan Talata a kan daukaka karar da jagoran wata kungiyar 'yan tawayen Kwango Bosco Ntaganda ya yi. 

Tun a shekarar ta 2019 ne dai kotun da ke birnin Hague ta same shi da laifukan da suka hada da kisa da cin zarafin mata da kananan yara  a lokacin da kungiyarsa ke tashen kaddamar da hare-hare a jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. A bisa wannan kotun ta yanke masa hukuncin shekaru 30 a gidan maza. 

Sai dai Ntaganda wanda tsohon janar ne na soja da ya rikide ya koma dan tawaye ya musanta zarge-zargen, inda lauyoyinsa suka ce kotun ta ICC ta tabka kurarai a cikin hukuncin nata.

A shekarar 2013 dakarun gwamnatin Kwango suka murkushe kungiyar 'yan tawaye ta M23 da Ntaganda ya jagoranta kuma a wannan shekara shi da kansa Ntaganda ya yi saranda inda ya mika kansa ga ofishin jakadancin Amirka da ke birnin Kigali na Ruwanda.