Hunkunci a kan wasu ′yan sanda a Masar | Labarai | DW | 04.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hunkunci a kan wasu 'yan sanda a Masar

Kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar Masar ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru goma na zaman gidan yari ga wasu 'yan sanda guda biyu.

Ägypten Proteste zum Jahrestag des Aufstands in Kairo 25.01.2015

Masu zanga-zanga a Masar

Kotun ta samu 'yan sandan da laifin kashe wani mai fafutuka mai yin rubuce-rubuce ta shafin Intanet na Blogs wato Khaled Said a shekarun 2010.

Mutumin da ake kallon a matsayin jigo wajen ƙaddamar da juyin juya halin da ya share gwamnatin Hosni Mubarak daga mulki a shekaru 2011.