Hulda tsakanin Jamus da Siriya na kara rauni | Labarai | DW | 10.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hulda tsakanin Jamus da Siriya na kara rauni

Jamus ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Siriya daga birnin Berlin na kasar.

Ma'aikatar kula da harkokin wajen Jamus ta fitar da wata sanarwa a wannan Litinin, inda ta bayyana korar wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Siriya hudu da ke birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus. Ma'aikatar ta ce daukar matakin na zaman wani bangare ne na rage huldarta da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya.

Ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerewlle ya fadi - cikin sanarwar cewar matakin, wani muhimmin sako ne ga shugaban na Siriya game da raunana alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewar Jamus za ta ci gaba da yin hulda tare da 'yan adawar kasar, wadanda ke samu karfi sannu a hankali.

Ma'aikatar kula da harkokin wajen na Jamus ta ce tuni ta sanar da mukaddashin jakadan Siriya a birnin Berlin game da matakin, kuma Jami'an diflomasiyyar na da wa'adin zuwa ranar Alhamis da ke tafe domin ficewa daga Jamus.

Tun cikin watan Mayu ne kasashen Jamus, da Faransa da Birtaniya, sai kuma Spain da Italiya suka kori jakadun Siriya daga kasashen su, bayan kissar kiyashin da aka yiwa mutane 100 a yankin Houla da ke arewacin birnin Homs.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas