Hukuncin kotu kan zaben Najeriya ya bar baya da kura | Siyasa | DW | 25.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukuncin kotu kan zaben Najeriya ya bar baya da kura

Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya biyu ne suka nemi kotun koli ta sake nazarin wasu jerin shari'u na zaben shugaban kasa dama na wasu gwamnoni jihohin kasar guda hudu.

Präsidentschaftswahlen Nigeria Muhammadu Buhari und Anhänger (picture-alliance/AP Photo/B. Curtis)

Jam'iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci sakamakon zaben da ya bai wa Buhari nasara

A wani abun da ke iya zama barazana ga tsarin shari'ar tarrayar Najeriya, manyan jam'iyyun kasar guda biyu sun nemi kotun kolin tarrayar Najeriya da ta sake nazarin wasu jerin shari'un da suka hada da har da ta zaben shugaban kasar da Muhammadu Buhari yayi nasara. Kama daga shari'ar zaben gwamnoni na jihohin Bayelsa da Imo da Zamfara da kuma Kano dabo, ya zuwa ita kanta shari'ar da ta tabbatar da Shugaba Buhari bisa mulkin tarrayar Najeriya, al'umma ta kasar suna ganin dabam a bangare na masu siyasa da ke neman kotun kolin da ta sake nazarin shari'un da ta yanke can baya.


Karikatur: Nigeria Politik (A. Baba Aminu)

Ana nuna wa juna yatsa kan sakamakon zabukan jihohi 4 da neman kotu ta sake nazari

Ko a ranar Litinin da ta gabata, an ruwaito jam'iyyar PDP ta adawa ta ce, za ta sake komawa kotun kolin da nufin ganin an sake kallon tsanaki bisa shari'ar ta shugaban kasa a karon farko a cikin tarihi na kasar. Kuma cikin tsakiyar sabon tsarin, wanda a fadar Senata Umar Ibrahim Tsauri da ke zaman sakataren jam'iyyar na zaman yadda suke kallon kokari na yanke hukunci iri biyu a bisa shari'a guda daya  a bangaren alkalan kotun.

Ko ya take shirin kayawa a gaban kotun dai tuni, ra'ayi ya zo kusan daya a tsakanin lauyoyi da ke kallon na dabaru na masu siyasar a matsayin sabon tsarin da ke iya komawa barazana mai girma a cikin tsarin shari'ar dama kila demokaradiyar tarrayar Najeriyar. Duk da tunani na kurarai na masu siyasar dai har ya zuwa yanzu kotun kolin na zaman matakin karshe na kwantar da hankula dama kara ginin tsari na demokradiya ta kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin