Hukuncin kisa ya hau kan sojojin Najeriya 12 | Siyasa | DW | 16.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukuncin kisa ya hau kan sojojin Najeriya 12

An yanke wa sojojin hukuncin ne bisa yi wa kwamandansu bore a Maiduguri cikin watan Mayun bana.

Wata kotun sojan da ta kamalla zamanta cikin daren jiya Litinin ne dai ta kai ga hukuncin da a cikinsa ta ce wani soja guda zai share shekaru biyu tare da yin aikin wahala, a yayin da ta sallami wasu 'yan uwansu biyar, kafin daga baya kotun mai wakilai guda Tara, ta yanke hukuncin da ke zaman babu zato.

To sai dai kuma tuni hukuncin ya fara jawo martani a sassa daban-daban na kasar da ake masa kallon marar kyau, ga kasar da ke tsakiyar yaki a yanzu. A fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman babban sakataren kungiyoyin farar hular yankin yammacin Afirka, wacce ke da cibiyarta a Abuja.

“Ai dokar soja ba dokar Allah ba ce, kuma ko dokar Allah akwai hanyoyi da tsari na aiwatar da ita. Saboda haka bai yi ba, ka yi zalunci kuma ka ce za ka tsawalla wa jama'a kan haka. Mutanen nan ba biyansu ake yi ba, ba kuma kula ake da su ba. A Najeriya ne kadai ake wannan, saboda manyan jami'an ne ke kwashe kudaden aikin''

Wannan ne dai karo na farko da kasar ta Najeriya ke shirin hallaka jami'an tsaron nata tun kusan shekaru 24 da suka gabata. A lokacin da tsohuwar gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta hallaka jami'an soja da dama, da aka samu da hannu da kokarin juyin mulkin watan Aprilun 1990 karkashin jagorancin Manjo Gedion Gwoza Orkar.

To sai dai kuma sabon hukuncin da ya zo tsakiyar yakin dai daga dukkan alamu, a fadar Dr Sadiq Abba da ke zaman wani masanin harkokin zamantakewar kasar ta Najeriya, na iya aika mugun sakon ga ragowar sojan da ke cikin yakin, dama abokan fadan su na kungiyar ta Boko Haramun.

“Wannan matakin da aka dauka ya bai wa kungiyar Boko Haram kwarin gwiwa, kuma zai rage kwarin gwiwar sojan Najeriya, sannan zai nuna wa duk duniya akwai matsala a tsakanin sojan Najeriya. Lallai basira za ta nuna cewar ba su shirya wa wannan yakin ba”

To sai dai kuma karkashin doka sojojin suna da damar daukaka kara, a karkashin dokar sojan kasar a wata kotu ta musamman da rundunar sojan kasar ke da iko na kafawa.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin