Hukuncin daurin rai da rai ga masu yunkurin juyin mulki
June 26, 2020Talla
Akalla mutane 245 ne kotun kasar ta tuhuma da yunkurin kifar da gwamnati, ciki har da wani babban kwamandan jami'an tsaron kasar, wadanda kuma za su shafe tsawon shekarun rayuwarsu a gidan yari, maimakon zartar da hukuncin kisa kansu biyo bayan soke dokar hukuncin a shekarar 2004.
Rahotanni sun yi nuni da cewa kimanin mutun 250 ne suka sulwanta a yayin yunkurin juyin mulkin na ranar 15 ga watan Yulin 2016, yankurin da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ta zargi malamin nan Fethullah Gülen da yanzu hakan ke samun mafaka a Amirka da kitsawa.