Hukunci kotu ya janyo zanga-zanga | Siyasa | DW | 06.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukunci kotu ya janyo zanga-zanga

Hukuncin daurin rai da rai da kotu ta yanke wa wasu manyan sojojin Turkiyya ya jawo martani daga al'umar kasa

Hukuncin da kotun kasar Turkiyya ta yanke na daure tsohon babban habsan sojoji na tsaron dai-da-rai, kan shari'a mai mai sarƙaƙiya ta mutane 275 waɗanda ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar. Wannan hukunci ya bar baya da kuri kuma ya zama zakaran gwaji ga gwamnatin kasar.

Shari'ar ta zama gagarumin kalubale ga Firaminista Recep Tayyip Erdogan da dangantakar gwamnatin da masu rajin kafa gwamnatin da ba ruwanta da addini da kuma dakarun sojin da ke adawa da shi. Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce an wanke 21 daga cikin waɗanda ake zargin, an kuma yankewa ɗaya daga cikin manyan tsoffin hafsoshin sojin ƙasar, Ilker Basbug hukuncin ɗaurin rai dai rai a gidan kaso tare da wasu jami'an sojoji, da wani hukuncin ɗaurin shekaru 35 wa wasu 'yan majalisa 'yan adawa su 12.

Yayin da aka sanar da hukunci an kai ruwa rana tsakanin masu zanga-zanga a wajen kotu da ke garin Silivri, da kuma 'yan sanda, wanda suka yi amfani da hayaki mai saka hawaye, domin tarwatsa wadanda suka fusata da hukuncin. Kakakin gwamnatin kasar ta Turkiya Bulent Arinc ya yi karin haske:

"A cikin mutane akwai sannannu wadanda suka rike makamai da suka hada da manyan hansoshin soji, wasu manyan ma'aikata ne. Amma tsarin shari'a babu nuna wani gata ga wanda ya aikata laifi. Kotu ta yanke hukuncin da ta ga ya dace bisa adalci. Babu murna da muke yi kan kama wani, amma wannan hukunci ne da kowa zai mutunta."

Tuni 'yan adawa da masu raji kare hakkin dan Adam suka yi tir da matakin na gwamnatin Turkiya, wanda suke dauka yunkurin na murkushe masu adawa da ita. Ahmet Sik dan jarida ne, wanda ya nuna bakin ciki da abin da ke faruwa a cikin kasar:

"Wannan a fayyace yake karara ana dakile 'yancin fadin albarkacin baki a Turkiya. Inda duk dan jaridar da ya yi suka zai iya rasa aikinsa ko kuma ya kare a gidan yari."

A birnin Ankara fadar gwamnatin kasar ta Turkiya daruruwan mutane sun fito kan tituna sun gudanar da zanga-zanga tare da cewa suna cikin sojoji Mustafa Kemal Ataturk, wato sojin da ya girka tsarin zamani na kasar ta Turkiya.

Wani gidan talabijin mai zaman kansa ya ruwaito cewa akwai mutane 15 da aka samu da laifi, amma an sake su nan take. Sannan wani dan majalisa na bangaren adawa Mehmet Haberal an rage tsawon hukunci da ana yanke masa, kuma tuni aka sake shi, saboda ya tsawon lokaci da yake tsare ya kai na zaman hukunci.

Tsohon babban habsan sojin kasar ta Turkiya, Ilker Basbug dan shekaru 70 da haihuwa, shi ne ya jagoranci rundunar sojan wajen kaddamar da yaki da 'yan awaren Kurdanawa na kungiyar PKK. Amma yanzu bayan ya yi murabus sai ga shi gwamnati ta tuhume shi da laifukan ta'adanci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin