Hukumar zaben Niger ta fara tattara sakamakon babban zaben kasar | Labarai | DW | 22.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zaben Niger ta fara tattara sakamakon babban zaben kasar

Hukumar ta CENI ta ce ana cigaba da gudanar da zabubbuka a wasu yankunan kasar da aka samu matsaloli da suka hada da jinkirin kai kayan zabe.

Jamhuriyar Niger wadda Allah ya huwace wa ma'adanun Uranium da kwal gami da mai al'ummar kasar sun kada kuri'unsu ne domin zabar shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin kasar a inda shugaba Mouhamadou Issoufou ke muradin ganin ya tsallaka zuwa wa'adin mulki na biyu.

Tun a ranar Lahadi dai al'ummar kasar suka futo kwansu da kwarkwata domin zaben wanda zai sake jagorantar kasar a shekaru biyar da ke tafe. An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a ta cewar hukumar zaben kasar wato CENI.

Sai dai 'yan jamiIyyun adawa sun sa kafa sun yi watsi da bullar sakamakon a inda suka ce an tafka magudi a cikinsa.

Mutane kimanin miliyan bakwai da dubu dari biyar suka cancanci kada kuri'a a kasar.