HRW ta bukaci MDD ta gudanar da bincike a Yemen | Labarai | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

HRW ta bukaci MDD ta gudanar da bincike a Yemen

Kungiyar Kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ta yi kira ga MDD da ta sake gudanar da wani aikin bincike kan batun cin zarafin biladama da bangarorin da ke yaki a kasar suka aikata.

Kungiyar Kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ta wasu kungiyoyi masu zaman kansu 56 sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta sake gudanar da wani aikin bincike kan batun cin zarafin biladama da bangarorin da ke yaki a kasar suka aikata.A cikin wata wasika da suka aika wa kasashe mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kungiyoyin sun bukaci a samar da wata kafa mai zaman kanta da za ta gudanar da aikin binciken cin zarafin dan Adam da aka aikata a wannan kasa ta Yemen inda a halin yanzu mutane sama da miliyan bakwai ke fuskantar barazanar yinwa a yayin da wasu rabin miliyan ke fuskantar barazanar cutar kwalara.